A Meta, muna jajircewa wajen ba wa mutane damar yin magana da kuma tsare su.
Hakan na nufin cewa muna cire bayanai masu cutarwa da suka saɓa wa dokokinmu, rage yaɗawa bayanai masu matsala waɗanda ba su saɓa wa dokokinmu ba, da kuma sanar da mutane ƙarin yanayi, ta yadda za su iya yanke hukunci a kan me za su danna, karanta ko raba.
1
Muna haɗa kai da ƙwararru na duniya a fannin fasaha da tsaron al’umma da haƙƙoƙin ɗan’adam don mu ƙirƙira mu kuma sabunta dokokinmu.
2
Muna samar da sigogi don tsaro, ta yadda mutane za su iya kai rahoton bayanai su kuma toshe su ko su ɓoye su ko su daina bin wani asusu.
3
Muna ɗabbaƙa dokokinmu ta amfani da fasaha da kuma mutane masu sake dubawa
Muna tsare mutane kuma muna ba su damar da za su iya kama mu da laifi ta hanyar sanar da dokokinmu da ɗabbaƙa su da rahoton tsage gaskiya.
Manufofinmu
Dokokinmu suna bayyana abin da aka yarda da wanda ba a yarda da shi ba a kan fasahohin Meta. Idan bayani ya saɓa wa dokokinmu, muna ɗaukar mataki a kansa.
Ɗabbaƙa Dokokinmu
Muna amfani da fasaha da kuma ma'aikatan dake sake dubawa don ganowa da sake dubawa da ɗaukar mataki a kan miliyoyin bayanai a kowace rana a Facebook da Instagram.
Rahotoninmu na tsage gaskiya
Muna wallafa rahotanninmu na tsage gaskiya na yau da kullum don nuna wa mutane abin da muke yi wajen ɗabbaƙa dokokinmu.
Hanyarmu ta yin bayanin matsayi
Tsarukan Ilimin gudanar da ayyuka ta kwamfuta suke samar da matsayin bayanai na sabo masu yawa akan kayayyakin Meta, kamar duba Ɓangaren Labarai na Facebook, kallon reels akan Instagram ko bincka Marketplace na Facebook.
Sabuntawar kwanan nan